Platini ya yabawa tawagar turai

Shugaban hukumar kwallon kafa ta turai
Image caption Yanzu ta tabbata cewa kasar Turai ce za ta lashe gasar ta bana

Shugaban hukumar kwallon kafa ta turai UEFA, Michel Platini, ya yabawa kasashen da ke wakiltar nahiyar a gasar cin kofin duniya da ake yi a Afrika ta Kudu, sakamakon rawar ganin da suke takawa.

A yanzu dai ta tabbata cewa za a kara wasan karshe ne tsakanin kasashen nahiyar Turai, bayan da Holland ta doke Uruguay, inda take jiran wanda zai samu nasara tsakanin Spaniya da Jamus.

Yace kasashen Holand da Spaniya da Jamus, wadanda suka lashe gasar matasa mafiya yawa a shekaru goma da suka wuce, duk sun samu kaiwa zagayen kusa da na karshe.

"Ko za a ce duka wannan sa'a ce kawai? A gani na zai yi wuya.

"Muna samun kyakkyawan tsari na ilimin zamani da tsarin gudanarwa mai kyau da ingantaccen shugabanci".

Da farko dai an zaci kasashen Kudancin Amurka ne za su lashe gasar bayan da Argentina da Brazil da Paraguay da kuma Uruguay suka halarci zagayen dab da na kusa da karshe.

Amma sai Brazil da sha kashi a hannun Holand, yayinda Argentina da Paraguay suka sha kashi a hannun Jamus da Spaniya.

Wanda hakan ya nuna cewa a karon farko za a samu wata kasar Turai da za ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a wajen nahiyar ta Turai.

"Wannan ba karamin abin farin ciki ba ne," a cewar Platini, shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai.