Waiwaye kan gasar cin kofin duniya ta bana

'yan wasan Spaniya na murna
Image caption 'yan wasan Spaniya suna murna bayan sun lashe Jamus a wasan kusa dana karshe

Wasan karshe na gasar cin kofin duniyar da za a fafata ranar Lahadi tsakanin kasashe biyu na Turai wato Holand da Spaniya, alamace ta yadda nahiyar ta mamaye gasar ta bana.

Duk da cewa da farko ana tunanin kasashen Kudancin Amurka ne za su lashe gasar, amma daga bisani sai labari ya sha ban ban.

Haduwar kasashen turai a wasan karshe wani abune da ba a zaci faruwarsa ba a farkon gasar.

Faransa da Italiya wadanda suka buga wasan karshe a gasar data gabata, sun kasa samun nasara a wasa ko daya, abin da yasa aka fitar da su a zagayen farko.

Image caption 'Yan wasan Uruguay na jimami bayan an fitar da su daga gasar

Itama Ingila bata kayatar da 'yan kallo ba, hatta Spaniya ma an doketa a wasan farko. Yayin da kasashen Afrika suma suka gaza, amma a bangare guda takwarorinsu na Kudancin Amurka suka rika taka rawar gani.

'Yan wasan Argentina sun ware nan da nan, inda suka rinka zira kwallaye. Alamu sun nuna Brazil ma ta samu kanta, tana da 'yan baya da kuma 'yan gaba sosai. Paraguay da Uruguay da Chile duk sun taka rawar gani a rukunansu.

A kasashen turai Jamus da Holand ne kawai suka nuna alamun za su iya yin wani abu na azo a gani a gasar.

Image caption 'Yan wasan Holand na taka rawar gani sosai a gasar ta bana

Amma sai al'amura suka sauya a lokaci guda. Kasashe hudu ne suka halarci zagayen dab dana kusa da karshe daga Kudancin Amurka, amma Uruguay ce kawai ta tsallake.

Masana sun yi maganganu da dama kan dalilan da suka sa kasashen Turai suka warware a gasar bayan sun yi lakolako a farko.

Spaniya da Holand basu kayatar da 'yan kallo da wata leda ta azo agani ba. Mai yiwuwa fahimtar juna da kuma sa'a ce ta taimaka musu.

Abin da ya fito fili dai a yanzu shi ne lallai daya daga cikinsu za ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihi.