An sabunta: 11 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 15:15 GMT

Karawa tsakanin Holland da Spaniya

A gasar da aka shirya a karo na farko a nahiyar Afrika za ta fito da kasa da ba ta lashe gasar ba ganin cewa kasashen biyu da za su buga wasan karshe ba su tabba daga kofin ba.

Babban tarihin da Spaniya ta taba kafawa a gasar shine a gasar da aka shirya a shekarar 1950 inda ta kare a matsayin ta uku.

Amma masana na yabawa da kwarewar da tawagar Spaniya take da shine cewa ganin cewa sun lashe wasanni hamsin cikin hamsin da hudu da suka buga karkashin jagoranci kocin su Vicente del Bosque.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Kasar Holland kuma ta buga wasan karshe ne a gasar da aka shirya a shekarar 1974 da kuma 1978. A yanzu haka dai ba a doke Holland din a wasanni ashirin da biyar da ta buga.

Daga wasanni share fage da Holland ta buga na halarta gasar cin duniya ya zuwa yanzu, kasar ta lashe duka wasanni da ta buga.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.