Tawagar Spaniya ta isa gida

Tawagar Spaniya ta isa gida
Image caption Wannan ne karo na farko a tarihi da Spaniya ta lashe gasar cin kofin duniya

Dubban jama'a ne suka taru afilin saukar jiragen sama na birnin Madrid domin yin maraba ga tawagar 'yan kwallon Spaniya bayan da suka isa gida daga Afrika ta Kudu inda suka lashe gasar cin kofin duniya.

Kyaftin din kasar Ike Casilas ne ya fara saukowa daga cikin jirgin inda yake rike da kofin, sannan sauran 'yan wasan suka biyo shi.

Firaministan kasar Zapatero, ya bayyana nasarar da suka samu da cewa wani abu ne da ba za a manta da shi a tarihin kasar ba.

Yayin da kociyan kasar Vicente Del Bosque, ya ce nasarar da kasar ta samu wata nasara ce ga kasaitacciyar ledar da suke takawa.

Wannan shi ne karo na farko da kasar ta lashe wannan gasar, kuma ta kafa tarihi ganin cewa itace ke rike da kanbun zakarun turai, wanda ta lashe a shekara ta 2008.

Daga bisani 'yan wasan sun garzaya zuwa cikin gari, inda dubban daruruwan jama'a suke jiransu domin yi musu maraba. Murna

An ci gaba da murna tun farkon dare har wayewar gari, inda jama'a suka yi ta shaye-shaye da kade-kade a Madrid babban birnin kasar.

Jama'ar wadanda suka rufe jikinsu da tutocin kasar sun rufe manyan titunan birnin na Madrid, abinda ya janyo tsaiko ga harkokin zirga zirga.

Har ila yau 'yan kasar ta Spaniya da ke zaune a kasashen duniya daban daban, da suka hada da Argentina da Amurka da Pakistan, sun yi ta murna suna shewa sakamakon wannan nasara.