Forlan ya fi kowa taka leda a gasar cin kofin duniya

Thomas Mueller
Image caption Thomas Mueller ya zira kwallaye biyar a gasar ta bana, sannan yasa aka ci kwallaye uku

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta bayyana dan wasan Uruguay Diego Forlan, a matsayin dan wasan da ya fi kowanne taka leda a gasar cin kofin duniya ta bana.

Dan wasan wanda ke taka leda a klob din Atletico Madrid ya zira kwallaye biyar, sannan ya taimakawa kasarsa ta kawo zagayen kusa da na karshe. Haka za lika dan wasan Jamus Thomas Mueller, ya lashe kyautar matashin dan wasan da ya fi kowanne taka leda a gasar.

Haka kuma hukumar FIFA ta bayyana Mueller, dan shekaru 20, a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallaye-bayan da ya zira kwallo biyar-sannan ya taimaka wajen zira kwallaye uku.

Dan wasan na Jamus ya doke Forlan da David Villa na Spaniya da Wesley Sneijder na Holand domin samun wannan kyauta, wadanda suma suka zira kwallaye biyar-biyar.

Image caption David Villa da Wesley Sneijder duka sun zira kwallaye biyar-biyar

Sannan ya doke dan wasan Mexico Giovani Dos Santos da na Ghana Andre Ayew, domin samun kyautar matashin dan kwallon.

Yayinda Forlan ya doke dan wasan Holand Sneijder da maki 23.4% a kuri'ar da 'yan jaridu na duniya suka kada, yayinda dan wasan Spaniya David Villa ya zo na uku.

"Wannan kyautar da aka bani godiya ce ga sauran 'yan wasanmu," a cewar Forlan, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter, inda ya ke dauke da hoton kyautar da aka ba shi.

Haka kuma an zabi mai tsaron gida na Spaniya Iker Casillas-wanda sau biyu yana hana Robben zira kwallo, golan da ya fi kowanne nuna bajinta a gasar, inda aka bashi kyautar safar zinare.