Fifa ta fito da jerin kasashen da suka taka rawar gani

Fifa ta fito da jerin kasashen da suka taka rawar gani
Image caption Tawar Spaniya ce ta daya bayan ta daga kofi

Hukumar kwallon kafa ta fito da jerin kasashen da suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.

Spaniya wanda ta lashe kofin ce ta daya a jerin kasashen, sannan Holland da ta buga wasan karshe ta zamo na biyu. Jamus ce dai ta uku. Ghana wanda ta buga wasan dab da kusa dana karshe a gasar ce ta zama ta bakwai.

Najeriya dai wanda bata lashe wasa ba a gasar kuma ta kare da maki guda a rukunin da ta buga ta na na ashirin da bawkwai ne cikin kasashe talatin da biyu da suka halarci gasar.

Najeriyar dai na gaban kasashe kamar su Algeria da Faransa da Honduras da Kamaru da kuma Koriya ta Arewa.

Jerin kasashen da suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniya

1 Spain, 2 Netherlands, 3 Germany, 4 Uruguay, 5 Argentina, 6 Brazil, 7 Ghana, 8 Paraguay

9 Japan, 10 Chile, 11 Portugal, 12 United States, 13 England, 14 Mexico, 15 South Korea, 16 Slovakia

17 Ivory Coast, 18 Slovenia, 19 Switzerland, 20 South Africa, 21 Australia, 22 New Zealand, 23 Serbia, 24 Denmark

25 Greece, 26 Italy, 27 Nigeria, 28 Algeria, 29 France, 30 Honduras, 31 Cameroon, 32 North Korea