Liverpool na da kwarin guiwa kan Torres

Fernando Torres
Image caption Fernando Torres ya dade yana fama da rauni a kakar wasanni ta bana

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ce tana da kwarin guiwar cewa raunin da Fernando Torres ya samu a gasar cin kofin duniya bai yi muni ba kamar yadda aka zata da farko.

Dan wasan na Spaniya-mai shekaru 26, wanda bai guga wasannin karshe na gasar Premier da ta gabata ba, ya samu rauni a gwuiwarsa a karshen wasan da kasarsa ta buga da Holand ranar Lahadi. Likitan klob din Peter Brukner, yace Spaniya ba ta saran raunin nada girma, amma za su jira har bayan aikin da za a yi masa tukunna.

A bangare guda kuma dan tsakiyar klob din Alberto Aquilani, ya warke daga raunin da ya ke fama da shi a idon sahun shi.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya koma Anfield daga Roma a watan Agustan shekara ta 2009, ya shafe watanni biyun farko ba ya taka leda.

Shi dai Torres ya dade yana fama da rauni tun kafin kirsimeti, abin da yasa aka yi masa aiki a kafarsa ta dama.

Aiki na biyu da aka yi masa a kafar ya sa shi kasa bugawa Liverpool wasanni hudu na karshen kakar wasan data gabata.

Kuma shi ne dalilin da ya hanashi taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu.