Chelsea na da kwarin gwiwa kan Mikel da Essien

Kungiyar Chelsea bayan ta daga kofin Premier a bara
Image caption Kungiyar Chelsea bayan ta daga kofin Premier a bara

Mataimakin kocin Chelsea Ray Wilkins ya ce kungiyar na da kwarin gwiwa cewa Michael Essien da John Mikel Obi za su buga wasa a farkon kakar wasan bana a ranar 14 ga watan Ogusta.

Essien dai yana fama da rauni ne a gwiwar sa tun a watan Junairun da ya gabata, yainda shima Mikel aka yi mai tiyata a kafarsa a watan Mayu.

"Ina ganin ba za mu fuskanci wata matsala ba," Inji Wilkins a lokacin da aka yimai tambaya kan 'yan wasan za su iya taka leda a wasan da kungiyar za ta buga da West Brom.

"John Obi ya fi samun lafiya amma dukansu suna samun sauki."

Ya kara da cewa: "Sun fara horo, kuma za su fara taka leda ba kakkautawa kafin a fara kakar wasan bana". Essien dai ya samu rauni a lokacin da ya tare da tawagar Ghana a gasar cin kofin Afrika, yayinda Mikel shima bai samu zuwa gasar cin kofin duniya ba saboda aikin tiyata da aka yi mai a gwiwar sa.