Ghana ta yunkuro sama a jerin kasashen da Fifa ta fitar

Tawagar Ghana
Image caption Tawagar Black Stars ta kasar Ghana

Tawagar Black Stars ta kasar Ghana ta dago sama daga 32 zuwa 23 a jerin kasashen da suka kware a harkar kwallon kafa da Hukumar Fifa ta fitar.

Ghanan dai ta buga wasan dab da kusa dana karshe ne a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu.

Harwayau dai kasar Masar ce kan gaba a nahiyar Afrika, yayinda Ghana take na biyu a nahiyar.

Ivory Coast dai ce ta uku a yayinda Najeriya take ta hudu.

Spaniya wanda ta lashe gasar cin kofin duniya ce ta daya a duniya a jerin kasashen da Fifa ta fitar.

Sai kuma Holland wanda aka doke ta wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta dago daga ta hudu zuwa ta biyu. Brazil dai wanda a baya ita ce na daya a duniya ta koma ta uku.

Tawagar Super Eagles dai ta Najeriya bayan mumunar ruwar da ta taka a kasar Afrika ta kudu ta sauko kasa ne a jerin kasashen duniya daga na 21 zuwa na 30 a duniya.

Kasar Afrika ta kudu ta fi kowace kasa dagowa sama inda ta dago daga ta 83 zuwa ta 66 a duniya.

Kasar Afrika ta kudu dai ce ta goma sha biyu a nahiyar Afrika.

Jerin kasashe goma a Afrika:

1. Egypt (9 duniya)

2. Ghana (23 duniya)

3. Ivory Coast (26 duniya)

4. Nigeria (30 duniya)

5. Algeria (33 duniya)

6. Gabon (34 duniya)

7. Cameroon (40 duniya)

8. Burkina Faso (45 duniya)

9. Mali (55 duniya)

10. Benin (61 duniya)