Henry ya bar Barcelona ya koma Amurka

Thierry Henry
Image caption Thierry Henry ya koma kungiyar Red Bull

Dan wasan Faransa da ke takawa kungiyar Barcelona leda Thierry Henry ya bar kungiyar ya koma taka leda a gasar Major League Soccer ta Amurka.

Dan wasan dai ya koma kungiyar New York Red Bulls ne a Amurka.

Tsohon dan wasan Arsenal mai shekarun haihuwa 32, zai fara takawa kungiyar Red Bull leda a wasan sada zumunci da za ta buga da kungiyar Tottenham ta Ingila a ranar 22 ga watan Yuli.

Henry ya ce: "Wannan yunkurin da nayi wani babban kalubale ga rayuwata da sana'ar kwallon kafa, kuma ina farin ciki da zuwa Amurka".