Najeriya ta buga kunnen doki da Ingila

Najeriya ta buga kunnen doki da Ingila

Najeriya ta buga daya da daya da Ingila a gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru ashirin da ake yi a kasar Jamus.

Kasashen biyu sun fafatane a rukunin C.

Ingila dai ce ta fara zura kwallon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, amm bayan an dawo sai Najeriyar ta fanshe.

Najeriya dai ta sama damar kara kwallo da dama amma ba ta iya zurawa ba.

Najeriya na rukunin C ne kuma za ta kece raini da Japan da Mexico bayan ta samu maki guda a karawar ta da Ingila