Capello zai gana da jami'an FA

Fabio Capello
Image caption Fabio Capello ya sha suka game da rawar da Ingila ta taka a gasar cin kofin duniya

Kociyan Ingila Fabio Capello zai dawo aiki a ranar Alhamis, inda zai tattauna da jami'an hukumar kwallon kafa ta kasar wato FA.

Kociyan zai gana da jami'an ne domin tattaunawa kan irin rawar da kasar ta taka a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Afrika ta Kudu.

Capello dan shekaru 64, ya rike aikinsa ne duk da mummunar rawar da 'yan wasansa suka taka, inda Jamus ta doke su da ci 4-1 a zagaye na biyu.

Itama dai hukumar ta FA wannan ne karo na farko da za ta gudanar da taro, tun bayan gasar ta cin kofin duniya.

Capello zai tattauna da shugaban hukumar Sir Dave Richards da kuma babban jami'in ta Alex Horne.

Shi dai Capello wanda dan kasar Italiya ne, ya yi alkawarin sauya fasalin kungiyar kwallon kasar domin mai da hankali kan matasa, kuma ana saran ganin hakan a lokacin da kasar za ta kara da Hungary a wasan sada zumunta a filin Wembley a ranar 11 ga watan Agusta.