Maradona zai ci gaba da horon Argentina

Diego Maradona
Image caption Diego Maradona

Rahotanni daga Argentina sun ce Diego Maradona zai ci gaba da jagoranci tawagar kasar har zuwa shekarar 2014 a lokacin da Brazil za ta karbi gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Maradona ya kai Argentina wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin duniya da aka kamala a kasar Afrika ta kudu.

Shugaban hukumar kula da kwallin kafa a Argentine Julio Grondona zai gana da Maradona domin tattaunawa kan kwantaragin sa.

Bayan da aka fidda Argentina ne a wasan dab da kusa dana karshe, Maradona ya ce ya duba yiwuwar ajiye aikin sa.