Henry ya daina takawa Faransa leda

Thierry Henry
Image caption Thierry Henry ya zira kwallaye 52 a wasanni 123 a Faransa

Dan wasan Faransa Thierry Henry, yace ya daina taka leda a gasar kasa-da-kasa bayan shafe shekaru goma sha uku ana fafatawa da shi.

Dan wasan mai shekaru 32, ya bayyana hakan ne kwana guda bayan ya sauya sheka daga Barcelona zuwa kungiyar New York Red Bulls ta Amurka.

Henry yace zai maida hankali kan sabon kolub din nasa, don haka ba zai so ya dinga zuwa nahiyar Turai akai-akai ba domin bugawa Faransa.

Dan wasan wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 1998, shi ne dan wasan da ya fi kowanne zira kwallaye a tarihin kasar, bayan da ya zira kwallaye 51 a wasanni 123.

Da yake magana a birnin New York a ranar Alhamis, Henry, wanda ya lashe gasar cin kofin turai da Faransa a shekara ta 2000, yace ya yanke shawarar ne tun kafin fara gasar cin kofin duniya da aka kammala a Afrika ta Kudu.

Tawagar Faransa sun yi wani bore inda suka ki yin atisayi kafin karawar su da Afrika ta Kudu, bayan da kociyan kasar ya kora Nicolas Anelka gidasaboda rashin da'a.

Wannan wasa dai shi ne na karshe da Henry ya taka, kamar yadda makamancinsa da suka yi da Afrika ta Kudu a 1997, ya zamo masa na farko da ya bugawa Faransar.