Cole ba na siyarwa bane- inji Ancelloti

Ashley Cole
Image caption Ashley Cole

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce dan wasan bayan kungiyar Ashley Cole ba zai bar kungiyar ba a kakar wasa mai zuwa.

Harwa yau dai kocin ya ce kungiyar ba ta nema siyan dan wasan Liverpool Fernando Torres kamar yadda ake ta yaya tawa a kafafen yada labarai.

Rahotanni dai na nuni da cewa kungiyar Real Madrid ta kasar Spaniya na neman siyan dan wasan amma Ancelotti ya ce: "Ina da kwarin gwiwa dari bisa dari cewa Cole na tare da mu a kakar wasa mai zuwa".

Kocin har ila yau ya ce kungiyar na da isasun 'yan wasan gaba domin haka ba ta bukatar siyan Torres.