Zanaco ta lallasa Eyimba 4-0

Zanaco ta lallasa Eyimba 4-0
Image caption Enyimba ce ta lashe gasar Premier a Najeriya

Kungiyar Enyimba da ta lashe gasar Premier a Najeriya ta sha kashi da ci hudu da nema a hanun kungiyar Zanaco ta kasar a gasar cin kofin Caf.Wasan da aka buga a birnin Lusaka, shine wasan da kungiyar Enyimba ta fi jin jiki a nahiyar Afrika.

Kungiyar Zanaco dai sun zura kwallayen hudu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kocin kungiyar Zanaco Wilson Nyirenda ya shaidawa BBC cewar duk da nasarar da kungiyar ta samu, 'yan wasan sun ji jiki.

"Buga wasa a gida na da wuya saboda akwai matsin lamba," Inji Nyirenda.

Mai magana da yawun kungiyar Enyimba Tonnex Chukwu ya alakanta rashin nasarar da kungiyar ta yi da kin nuna kishi ga wasu daga cikin 'yan wasan kasar.

"muna da matsalolin cikin gida," said Chukwu.

"Ranar da mu ka lashe gasar Premier a Najeriya 'yan wasan mu ficewa su ka yi daga sansanni horon su.".

Harwa yau dai Chukwu ya ba wa magoya bayan kungiyar cewa kungiyar za ta magance duk wa ta matsala da ke damin ta domin tunkan wasanni na gaba.

A sauran wasanni da aka buga a gasar a karshen mako kungiyar Sudan's Al Ittihad ta kasar Sudan ce ta doke Primeiro de Agosto ta kasar Angola da ci biyu da nema.

Ita kuwa kungiyar Gabaronne United ta kasar Botswana ta doke Haras el Hodoud ta kasar Masar da ci daya mai ban haushi, yayinda kungiyar Petro Atletico Luanda ta kasar Angola ta buga canjaras da kungiyar Club Sportif Sfaxien ta kasar Tunisia.