Al Ahly ta buga kunnen doki da Heartland

Kocin Heartland Samson Siasia
Image caption Kocin Heartland Samson Siasia

Kungiyar Al Ahly ta kasar Masar ta rike kungiyar Heartland ta Najeriya inda kungiyoyin biyu su ka tashi kunnen doki wato daya da daya a gasar zakarun Afrika.

Dan wasan Enyimba Bello Musa Kofarmata ya fara zura kwallon farko, sanan Mohamed Aboutrika ya fanshewa Al Ahly.

Samson Siasia ne ya jagoranci kungiyar Heartland a wasan bayan nadin da aka yi mai a makon da ya gabata.

Sauran kungiyoyin da ke rukunin B sun hada da Ismaili ta kasar Masar da kuma JS Kabylie ta kasar Algeria.

Heartland ta barar da kwallaye da dama a wasan, amma ta samu zura kwallon ne bayan minti hudu da aka dawo daga hutun rabin lokaci.