TP Mazembe ta doke Dynamos

Mai rike da kambun gasar zakarun Afrika TP Mazembe ta kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta doke kungiyar Dynamos ta kasar Zimbabwe da ci 2-0 a wasan farko da kungiyoyin biyu su ka buga a rukunin A, a gasar ta bana.

Dan kasar Zambia da ke takawa kungiyar Mazembe leda Given Singuluma ya zura kwallayen biyu a wasan.

Mazembe dai ce tafi rike kwallo a wasan, a yayinda kungiyar Dynamo ba ta kai wani hari na a zu agani ba a wasan.

"Muna matukar farin cikin ganin cewa munyi nasara a kan kungiyar Dynamos, kuma a yanzu haka muna da sauran wasanni biyu a gida, wanda kuma zammu nemi mu lashe" inji kocin Mazembe Diego Garzitto.

"Mun dan yi wasu kura kurai a wasan amma za mu yi kokari mu ga hakan ba sake aukuwa ba".

Kocin Dynamos Elvis Chiweshe ya shaidawa BBC cewar yana da kwarin gwiwa cewa kungiyar za ta taka rawar gani nan gaba a gasar.