Casillas ya yaba da shirye shiryen Mourinho

Iker Casillas
Image caption Casillas ne kyaftin din Spaniya

Mai tsaron gidan Real Madrid Iker Casillas ya yaba da kamun ludayin sabon kocin kungiyar Jose Mourinho yayinda ake shirin fara kakar wasa mai zuwa a gasar laliga ta kasar Spaniya.

Casillas ne dai ya jagoranci tawagar Spaniya a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda kasar ta lashe gasar.

Casillas dai ya ce hankalin sa ya koma gasar ta laliga, kuma ya ce yana fatan sauran 'yan wasan kungiyar za su ba sabon kocin kungiyar hadin kai.

Ya kamata dai 'yan wasan Madrid da su ka taka leda a gasar cin kofin duniya su dawo kungiyar a ranar tara ga watan Augusta amma sabon kocin kungiyar ya nemi 'yan wasan da su dawo mako guda kafin ranar.

Casillas dai ya ce ya amince da bukatar Mourinho kuma yana fatan sauran 'yan wasan za su bada hadin kai, kuma kada su bari murnar cin kofin duniya ya sa su mance da aikin da ke gaban su.