Liverpool ta sayi Joe Cole

Liverpool ta sayi Joe Cole
Image caption Joe cole ya takawa Chelsea leda na tsawon shekaru bakwai

Kungiyar Liverpool ta kammala siyan Joe Cole na tsawon shekaru hudu bayan dan wasan ya bar kungiyar Chelsea.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 28 ya baro kungiyar Chelsea ne bayan sun kasa cimma matsaya game da sabon kwantaragin sa.

Cole, dai ya yi shekara bakwai ya na takawa Chelsea leda, kuma kafin Liverpool din ta saye shi kungiyoyi kamar su Arsenal da Tottenham.