Semenya ta lashe tseren mita 800 a karo na biyu

Semenya ta lashe tseren mita 800 a karo na biyu
Image caption Caster Semenya

'Yar tseren kasar Afrika ta kudu Caster Semenya ta lashe tseren mita 800 a karo na biyu cikin kwanaki hudu, bayan ta dawo tseren sakamakon gwajin jinsin da aka yi mata.

Caster Semenya dai ta ce duk da ta dauki tsawon lakaci ba ta yi tseren ba, a yanzu haka ta kara sauri a kan da.

'Yar tseren duniyan ta dauki tswon minti biyu da dakikai arba'in da daya a gasar Savo a Lapinlahti, a kasar Finland.

"Na samu abin da nake nema saboda ya kara sauri". inji Semenya.

'Yar kasar Sweden Sofia Oberg ta kare a matsayin ta biyu, yayinda 'yar Rasha Anna Verkhovskaya ta zama ta uku.