Zan ci gaba da takawa Liverpool leda- Inji Gerrard

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard

Kyaftin din kungiyar Liverpool Steven Gerrard ya bada tabbacin cewar zai ci gaba da takawa kungiyar Liverpool leda a yayinda yakewa Joe Cole maraba da zuwa kungiyar.

An ta yayatawa cewar dan wasan zai bar kungiyar, amma bayan tattaunawar da ya yi da kocin kungiyar Roy Hodgson, dan wasan ya nuna cewa ya so ya ci gaba da zama a kungiyar.

"Mun sadu da Roy Hodgson a sirrance," inji dan wasan a wani bayani da ya yi a shafin intanet din kungiyar.

"Bayan mun tattauna, nayi kuma farin ciki da shirin da ya shimfida ya farfado da martaban kungiyar".

Ya kara da cewa: "Na dawo horo ranar litini, kuma na zaku a fara sabon kakar wasanni".

Rahotanni a baya dai sun ce sabon kocin Real Madrid Jose Mourinho na neman ya sayi dan wasan.