Oosthuizen ya ce Gary Player ne ya ba shi kwarin gwiwa

Louis Oosthuizen ne ya lashe gasar Open ta bana
Image caption Louis Oosthuizen ne ya lashe gasar Open ta bana

Dan wasan Golf din kasar Afrika ta kudu Louis Oosthuizen ya ce shahararen dan wasan Golf din Gary Player ne ya kara masa kwarin gwiwan a wani hira da suka yi ta wayar tarho wanda kuma ya ya yi nasara a gasar Open da aka kammala a karshen mako.

Ya ce; "munyi hira a harshe na Afrikana, inda tsohon dan wasan ya ce in kwantar da hankali ne, in yi wasa, ya kuma bani labarin lokacin da ya buga da Arnold Palmer, inda babu wanda ya dauko zai iya tabuka koma, amma daga bayan sai ya yi galaba a kansa.A gaskiya wadanan kalamu sun dadamini rai".

Louis Oosthuizen ya ce ba zai yi takara ba a gasar US Open duk da cewa dai yana da 'yan cin ya yi hakan, ya ce zai ci gaba da wasa ne a Turai