Arsenal da Tottehham sun hana amfani da Vuvuzela

Vuvuzela
Image caption Vuvuzela

Arsenal ta bi sahun kungiyar Tottenham inda ta hana 'yan kallo hura kakakin vuvuzela a lokacin da ake wasa.

Masoya kwallon kafa sun yi amfani da kakakin ne a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka kammala a kasar Afrika ta kudu, wanda kuma tuni hukumomi a wasu manya gasa a duniya su ka hana amfani da kakakin saboda karar da ta ke yi.

Kungiyar Arsenal ta ce tana so ta tabbatar "tsaro da kuma jindadin 'yan kallo ne".

Kungiyar Tottenham dai ta dau matakin ne bayan ta tattauna da jami'ain 'yan sanda da kuma jami'ain kiwon lafiya, inda su ka bada shawarar hana amfani da kakakin bisa dalilin cewa karar kakakin na iya kawo matsala ga tsaron lafiyar jama'a.