Ronaldinho ba na sayarwa bane: in ji AC Milan

Dan wasan AC MIlan Ronaldinho
Image caption Ronaldinho ya shahara wajen taka leda a baya

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Silvio Berlusconi, ya ce kungiyar ba za ta sayar da shahararren dan wasan ta Ronaldinho ba.

Mista Berlusconi ya ce idan har dan wasan zai ci gaba da taka tamaula, to zai ci gaba da kasance wa a kungiyar.

A shekara ta 2005 ne Ronaldinho ya sami kyautar kasancewar dan wasan da ya fi iya taka leda a duniya, lokacin da yake klob din Barcelona, yayinda kungiyar ta lashe kofin zakarun Turai.

Kafin daga bisani ya koma AC Milan akan Euro miliyan 18.5, sai dai bai samu damar haskakawa a gasar seria A ba, kamar yadda a ka zata.

Kungiyar AC Milan dai ta kammala gasar seria A ta bana ne a matsayi na uku a tebur.