Eduardo ya koma Shakhtar Donetsk

Eduardo
Image caption Eduardo da Silva

Dan wasan kasar Croatia da ke takawa Arsenal leda Eduardo ya koma kungiyar Shakhtar Donetsk ta kasar Ukraine.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 27 ya sa hanu ne a kwantaragin da zai sa ya takwa kungiyar leda na tsawon shekaru hudu a kan kudi fam miliyan shida.

Arsenal ta sayi Eduardo ne daga kungiyar Dinamo Zagreb a shekarar 2007 wanda kuma ya sa bai buga wasa ba na tsawon shekara guda saboda karaya da ya yi a kafarsa a shekarar 2008.