NFF za ta dauki mataki a kan Lagerback

Lars Lagerback
Image caption NFF ta dauki Lagerback na tsawon gasar cin kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya wato NFF ta ce za ta bayana matakin da ta dauka game da kocin Super Eagles Lars Lagerback.

Duk da dai cewa Najeriya ba ta lashe wasa ko guda ba a gasar cin kofin kwallon kafa da aka kammala a kasar Afrika ta kudu, hukumar na nema daukan mai horas a 'yan wasan na tsawon shekaru hudu.

Kocin mai shekarun haihuwa 62 har yanzu dai bai amince da neman da hukumar ke yi masa ba, idan kuma ya bukaci lokaci domin ya tattauna da iyalinsa a kasar Sweden.

A baya dai an yi hasashen cewar hukumar tA NFF ba za sake daukan Lagerback aiki ba saboda an samu sauyi a shugabancin kungiyar.

Mai magana da yawun hukumar Mista Ademola Olajire ya ce hukumar ba ta so ta dauki wani mataki cikin hanzari.

Olajire ya ce hukumar ta ba Lagerback lokaci "domin ya kara tunani game da yiwuwar aiki da mu".

Ya ce kungiyar za ta dauki mataki game da wani sabon koci a mako na gaba.

Kwantaragin Lagerback zai kare ne a karshen watan Yulin nan, kuma Najeriya za ta fara buga wasannin share fage na taka leda a gasar cin kofin Afrika a watan Satumba.