Fedrigo ya lashe zagaye na 16 a gasar Tour de France

Lance Armstrong
Image caption Lance Armstrong ya lashe gasar Tour de France sau bakwai

Pierrick Fedrigo ne dai ya sha gaban Lance Armstrong inda ya lashe zagaye na goma sha shida a gasar.

Armstrong ya lashe gasar ta tour de france har sau bakwai a baya amma Fedrigo ya hana zakaran gasar ne nasara da wani dan tazara.

Har wa yau dai Alberto Contador ne kan gaba a gasar gabaki daya a yayinda Andy Schleck ya ke na biyu.