Za a kara alkalan wasa a gasar zakarun Turai

Alkalan wasa
Image caption An yi amfani da alkalan wasa hudu a gasar Europa a bara.

Hukumar gudanarwa ta kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa IFAB ta ce za a samu karin alkalan wasa biyu a gasar zakarun Turai daga badi.

A bara dai an yi amfani da karin alkalan wasa biyu a gasar Europa, kuma hukumar ta ce kari alkalan wasan zai taimaka kwallon kafa

Hukumar kwalln kafa ta duniya wato FIFA ta ce za ta lurra da gwajin amfani da karin alkalan wasan a gasar zakarun Turai, inda kuma ce idan shirin ya yi tasiri za ta duba yiwuwar amfani da shi a manyan gasa a duniya.

Hukumar ta IFAB ta ce za ta tattauna batun amfani da na'uran zamani wajen tantance shigar kwallo raga a taron da za ta yi a watan Okutoba.

Sauran manya gasa a nahiyar Asia da kuma kudancin Amurka na duba yiwuwar amfani da karin alkalan wasa.