Najeriya ta gayyaci 'yan wasa 35

Mikel Obi
Image caption Mikel Obi bai taka leda a gasar cin kofin duniya da ta gabata ba

Najeriya ta gayyato 'yan wasa 35 domin yin horo game da wasan sada zumuntar da kasar za ta buga da Koriya ta Kudu a ranar 11 ga watan Agusta.

Daga cikin 'yan wasan da kasar ta gayyata har da Mikel Obi, wanda rauni ya hana shi taka leda a gasar cin kofin duniya da a ka kammala a Afrika ta Kudu.

Tawagar wacce mataimakin kociyan Super Eagles Austin Eguavoen, ya gayyato, ta kunshi 'yan wasan da ke taka leda a gasar Premier ta Najeriya da dama.

Eguavoen ne dai ke jagorantar kungiyar kafin a fayyace makomar kociya Lars Lagerback.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce, za ta yanke hukunci a kan makomar Lars Lagerback a mako mai zuwa.

Har ila yau tawagar ta kunshi Ikechukwu Uche da Joseph Akpala, wadanda aka a jiye lokacin gasar cin kofin duniya.

Amma abin da zai ja hankalin mutane shi ne na rashin gayyatar Sani Kaita, wanda ya samu jan kati a gasar cin kofin duniya.

Wasan sada zumuntar dai wani bangare ne na shirye-shiryen kasar domin tunkarar wasan neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika, da za ta kara da Madagascar a ranar 4 ga watan Satumba a Abuja.

'Yan wasan waje

John Obi Mikel (Chelsea, England), Dickson Etuhu (Fulham, England), Kalu Uche (Almeria, Spain), Osaze Odemwingie (Lokomotiv Moscow, Russia), Obinna Nsofor (Malaga, Spain), Haruna Lukman (Monaco, France), Ikechukwu Uche (Zaragoza, Spain), Obafemi Martins (Rubin Kazan, Russia), Ayodele Adeleye (Sparta Rotterdam, Netherlands), Daniel Shittu (Bolton Wanderers, England), Vincent Enyeama (Hapoel Tel Aviv, Israel), Elderson Echiejile (Sporting Braga, Portugal), Joseph Akpala (FC Brugge, Belgium).

'Yan wasan gida

Bassey Akpan (Bayelsa FC), Terna Suswam (Lobi Stars), Valentine Nwabili (Enyimba FC), Gabriel Reuben (Enyimba FC), Promise Onuh (Tornadoes FC), Ahmed Musa (Kano Pillars), Solomon Okpako (Kano Pillars), Uche Nwofor (3SC), Gbolahan Salami (Sunshine FC), Taiwo Hassan (3SC), Eugene Salami (Tornadoes FC), Chigozie Agbim (Warri Wolves), Moses Bunde (Lobi Stars), Nnaemeka Anyanwu (Enyimba FC), Emmanuel Anyanwu (Enyimba FC), Chidiebere Okoli (Sharks FC), King Osanga (Heartland FC), John Owoeri (Heartland FC), Femi Balogun (Kaduna United), Ugwu Uwadiegu (Rangers FC), Suleiman Ismaila (Lobi Stars), Fengor Ogude (Warri Wolves).