Liverpool za ta kara da Rabotnicki a gasar Europa

Kociyan Liverpool Roy Hodgson
Image caption Wannan shi ne zai zamo wasan farko na wata gasa ga Kociya Roy Hodgson

Liverpool za ta kara da Rabotnicki a zagaye na uku na gasar share fagen shiga gasar Europa, bayan da Rabotnickin ta doke Mika da ci daya mai ban haushi.

Kungiyoyin biyu sun tashi canjaras ne a wasan farko da suka kara.

Yayinda Shamrock Rovers na Dublin za su kara da Juventus na Italiya, bayan da suka doke Bnei Yehuda na Isra'ila da ci biyu da daya.

Motherwell na Scotland za su kara da Aalesund na Norway bayan da suka lashe Breidablik na Iceland da ci 2-0, bayan kammala wasanni biyu.

Bangor City na Wales za su kara da Maritimo na Portugal, yayinda Cliftonville za ta kara da CSKA Sofia na Bulgariya.

Za dai a buga wasannin ne a ranakun 29 ga watan Yuli da kuma 5 ga watan Agusta.