Mano Menezes ne sabon kocin Brazil

Menezes
Image caption kocin Brazil Mano Menezes

Hukumar kwallon kasar Brazil ta nada Mano Menezes a matsayin kocin 'yan kwallon kasar.

Menezes ya amince ya jagoranci Brazil zuwa gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014 da zata dauki bakunci.

Tun bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu ne Brazil ta kori kocin 'yan kwallonta Carlos Dunga saboda rashin taka rawar gani a gasar.