Maradona zai cigaba da zama kocin Argentina

Maradona
Image caption Kocin Argentina Diego Maradona

Diego Maradona ya ce yanason ya cigaba da zama mai horadda 'yan kwallon kasar Argentina amma sai idan har za a barshi ya cigaba da aiki tare da sauran mataimakanshi.

Shugaban hukumar kwallon Argentina Julio Grondona ya ce yana saran Maradona zai kulla wata sabuwar yarjejeniya da kasar daga nan zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Amma dai Grondona ya soki mataimakin Maradona Oscar Ruggeri bisa wasu dalilai.

Sai dai Maradona din ya shaidawa wata tasha talabijin cewar idan har aka kori daya daga cikin mataimakanshi tabbas zai ajiye aikin.

An dai soki Maradona bayan fidda Argentina a gasar cin kofin duniya ta bana inda Jamus ta lallasa ta daci hudu da nema a zagayen gabda na kusada karshe.