Har yanzu Ballack na murmurewa

Micheal Ballack
Image caption Rauni ne ya hana Micheal Ballack zuwa Afrika ta Kudu

Kociyan Bayern Leverkusen Jupp Heynckes, ya ce Ballack na ci gaba da murmurewa don haka ba zai takawa Jamus leda a wasan da za ta buga da Denmark ba.

Ballack wanda ya fara atisayi a sabon klub din da ya koma makon da ya gabata, kociyan na ganin ya yi wuri ya fara taka leda.

"Zai iya zamowa ganganci idan muka barshi ya taka leda a wasan sada zumuntar da Jamus za ta kara da Denmark a ranar 11 ga watan Agusta," in ji Heynckes

Dan wasan mai shekaru 33, ya samu rauni a idan sahun shi, abin da kuma ya hanashi taka leda a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu.

Kociyan Jamus Joachim Loew, a makon da ya gabata ya bayyana cewa zai tattauna da Ballack game da makomarsa a tawagar kasar.

Jamus dai ta taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da ta gabata.