Inter Milan ta karbi tayin Real Madrid akan Maicon

Maicon
Image caption Dan Brazil Maicon

Kungiyar Inter Milan ta amince da tayin da Real Madrid ta yi mata akan dan kwallon Brazil Maicon

Rahotanni sun nuna cewar Real Madrid zata bada Euro miliyan 28 don Inter Milan ta bar mata Maicon.

Koda yake dai ba a kamalla yarjejeniyar ba, amma dai ana saran Maicon din zai hade tsohon kocinsa Jose Mourinho.

Babban takaddamar da ake yi shine Maicon na bukatar a bashi Euro miliyan shida a kowace shekara a yayinda shi kuma shugaban Real Florentino Perez yace zai ba dan kwallon Euro miliyan biyar da rabi.