West Ham: Parker ba na sayarwa bane

Scott Parker
Image caption Scott Parker yana taka rawar gani a West Ham

Kungiyar West Ham ta Ingila ta yi watsi da bukatar kungiyar Tottenham na sayen dan wasanta Scott Parker.

Dan wasan na Ingila mai shekaru 29, wanda ke da sauran shekaru uku a kwantiraginsa, ana danganta shi da yiwuwar barin kungiyar ta West Ham.

Amma shugaban kungiyar David Sullivan, ya bayyana cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne akan kowanne irin farashi.

"Na yi alkawarin ba zan sayar da Scott ba, kuma ina nan kan bakana," kamar yadda ya shaidawa shafin intanet na kungiyar.

A baya West Ham ta sha sayar da 'yan wasa, amma yanzu zamani ya sauya, lokaci ne na fada da cikawa.

"Wannan sabuwar West Ham ce, muna kokarin tabbatar da ci gaban kungiyar, kuma idan muka yi alkawari to za mu cika," in ji David Sullivan.