Hughes ne zai zama kocin Fulham

Mark Hughes
Image caption Mark Hughes ya taba takawa kungiyar Manchester United da kuma Chelsea leda

Fulham ta cimma yarjejeniya da tsohon kocin Manchester city, Mark Hughes domin zama kocin kungiyar.

Kungiyar ta ce nan da kawanaki biyu ne za ta bayana Mark Hughes a matsayin kocin kungiyar a hukumance.

Mark Hughes mai shekaru 46, ya taba takawa kungiyar Manchester United da kuma Chelsea leda a baya, kuma bai samu aiki ba tunda kungiyar City ta sallame shi a watan Disamban 2009.

Kocin zai maye gurbin Roy Hodgson, wanda ya koma kungiyar Liverpool.

Fulham dai a baya ta nemi ta dauki kocin Ajax Martin Jol aiki amma ba ta samu cimma matsaya da kungiyar Ajax ba.