Esperance da JS Kabylie sun haskaka a Afrika

caf
Image caption Tambarin gasar CAF

Kungiyar Esperance ta Tunisa ta dauki gagarumin matakin tsallakewa zuwa zagayen kusada karshe na gasar zakarun kwallon Afrika bayan ta doke Dynamos ta Zimbabwe daci daya me ban haushi.

Dan kwallon Esperance Oussama Darragi shine yaci kwallon a bugun penariti, nasarar data baiwa Esperance din maki shida.

Itama JS Kabylie ta kasar Algeriya ta doke Heartland ta Najeriya da ci daya da nema.

Kabylie a yanzu tana da maki shida cikin karawa biyu data yi a rukunin B,kamar yadda Esperance ma keda maki shida.