'Yan matan Jamus sun doke Najeriya

falconets
Image caption Falconets na Najeriya

Jamus ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta mata 'yan kasada shekaru 20 bayan ta doke Najeriya daci biyu da nema.

Alexandra Popp da Kim Kulig ne suka ciwa Jamus kwallayenta biyu.

Hakan na nufin cewar Jamus ta lashe gasar sau biyu kenan bayan ta daga kofin a kasar Thailand a shekara ta 2004.

Najeriya ta kasance kasar Afrika ta farko data kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasada shekaru 20.