Mesut Özil yananan daram a Werder Bremen

Mesut Özil
Image caption Dan kwallon Jamus Mesut Özil

Dan kwallon Werder Bremen Mesut Özil ya ce ba zai sauya sheka ba don ya bar kungiyar a bana.

Wannan matakin dai ya kawo karshen zawarcin da wasu manya manyan kungiyoyi na Turai ke yi akan shi.

Rahotanni sun nuna cewar kungiyoyin Manchester United da Arsenal da Tottenham Hotspur da Real Madrid duk sun kwadayin sayen Özil.

Amma dai dan kwallon mai shekaru 21 ya hakikance ba zai bar Bremen ba, har sai yarjejeniya tsakaninsu ta kare a karshen kaka mai zuwa.