Song ya yi ritaya daga bugawa Kamaru

Song
Image caption Tsohon kaptin din Rigobert Song

Tsohon kaptin din Indomitable Lions na Kamaru Rigobert Song ya sanarda cewar ya yi ritaya daga bugawa kasar kwallo.

Dan shekaru 34 da haihuwa, Song ya bugawa Kamaru wasanni 138 kuma ya kasance dan Afrika na farko daya taka leda a gasar cin kofin duniya daban daban guda hudu.

Bugu da kari Song ya buga wasanni 33 a gasar cin kofin kasashen Afrika inda suka daga kofin a shekara ta 2000 da kuma 2002.

A baya Song ya taba bugawa Liverpool da West Ham da Metz da Cologne da Lens.