FIFA ta baiwa Sudan wa'adin makwanni biyu

Blatter da Valcke
Image caption Shugaban FIFA Sepp Blatter da Sakatare Janar Jerome Valcke

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa hukumar kwallon Sudan makwanni biyu ta zabi sabbin shugabaninta masu cin gashin kansu ko kuma a dakatar da Sudan din daga shiga gasar kwallo a duniya.

FIFA a ranar litinin ne ta rubutawa Sudan wasikar cewa bata gamsu da zaben da aka gudanar a makon daya gabata ba, kuma daga nan zuwa ranar 15 ga wannan watan ayi sabon zabe ko kuma ta fuskanci hukunci.

A dokokin FIFA dai, an haramtawa gwamnati tsoma baki a harkar kwallon kafa, kuma idan har 'yan siyasa suka saka hannu cikin lamarin, tabbas kasar zata iya fuskantar dagewa daga harkokin wasanni.