Utaka na shirin komawa Blackburn Rovers

John Utaka
Image caption Dan Najeriya John Utaka

Akwai alamun cewar Shugaban kungiyar Blackburn Rovers ta Ingila John Williams na zawarcin dan kwallon Najeriya John Utaka daga Portsmouth.

Portsmouth dai na shirin sayar da dan kwallon Najeriyan ne saboda ta fita daga gasar Premier ta koma nationwide.

Kungiyoyin kamarsu Bolton da Sunderland da Fulham duk suna kwadayin sayen dan kwallon mai shekaru 28,amma dai bisa dukkan alamu yinkurin Rovers ya fi na sauran.

Ita dai Portsmouth na fama da bashi rututu akanta kuma rabuwa da manyan 'yan kwallonta zai taimaka wajen rage kashe kudi.