Mun kosa Fabregas ya koma Barca-Iniesta

Iniesta
Image caption Kwallon da Iniesta yaci a gasar cin kofin duniya

Andres Iniesta ya hakikance duka 'yan wasan Barcelona na son kaptin din Arsenal Cesc Fabregas ya koma taka leda a Camp Nou.

Barca dai ta nuna maitarta a fili na sayen Fabregas, amma dai Arsenal ta cika kudi akanshi kuma bata son rabuwa dashi.

A yayinda ya rage kasada wata guda a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo, Iniesta na fatar ganin cewar kungiyoyin biyu sun sasanta akan Fabregas.

Iniesta yace"Dukanmu na son yazo saboda zai taimaka mana matuka".

A cewar Iniesta hada David Villa da Cesc Fabregas zai kara karfin Barca.