Chelsea za ta sayi Ramires

Ramires
Image caption Dan kwallon Brazil Ramires Santos do Nascimento

Chelsea na saran za ta sayi dan kwallon Brazil Ramires daga Benfica akan pan miliyan 17.

Matashin mai shekaru 23 a ranar laraba ake saran Chelsea za ta gwada lafiyarshi.

Ana saran Ramires zai kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru hudu da Chelsea kafin karshen wannan makon.

Dan kwallon wanda cikakken sunanshi Ramires Santos do Nascimento ya samu yabo daga wajen Dunga lokacin gasar cin kofin duniya.

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti na kokarin kara karfin tsakiyarshi saboda ficewar Joe Cole da Michael Ballack da kuma Deco.