Robben ba zai taka leda ba na wattani biyu

Robben
Image caption Dan kwallon Holland Robben

Zakaran gasar Jamus Bayern Munich ta gamu da cikas saboda dan wasan data fi ji dashi Arjen Robben ya samu rauni a cinyarshi.

Robben zai shafe watanni biyu kafin ya murmure abinda kuma hakan zai iya jawowa Bayern cikas a yinkurinta na kare kofin data lashe a kakar wasan data wuce.

Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya nuna takaici akan raunin, inda yace bai kamata Robben ya bugawa Holland wasan karshe a gasar cin kofin duniya ba saboda rauni.

Robben dai ya taimakawa Bayern ta lashe gasar Bundesliga dana FA sannan kuma aka doke ta a wasan karshe na gasar zakarun Turai.