Abinda yasa Joe Cole ya bar Chelsea- Ancelotti

Cole
Image caption Tuni har Joe Cole ya hade da sauran 'yan Liverpool

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce zuwan Yossi Benayoun ne makwafin Joe Cole a kungiyar.

Cole ya kulla yarjejeniya da Liverpool bayan Chelsea ta amince ya tafi sakamakon kasa sasantawa tsakaninsu, a yayinda shi kuma Benayoun ya bar Liverpool ya koma Chelsea.

Ancelotti yace "Joe Cole a lokacin yana Chelsea dan wasa ne na gani na fada,amma a shekara gudan data wuce labarin daban ne".

Joe Cole dai ya yi fama da rauni a gwiwarshi a kakar wasan data wuce, amma bayan zuwan Ancelotti ya sha jinjina sosai.