Sunderland na son golan Manchester City

Joe Hart
Image caption Golan Manchester City Joe Hart

Sunderland na son ta sayi golan Manchester City Joe Hart na wucin gadi.

Kocin Sunderland Steve Bruce na son wanda zai maye gurbi golanshi wanda ya turgude Craig Gordon.

Hart me shekaru 23 a karshen kakar wasan data wuce dai ya koma Birmingham ne na wucin gadi.

Bruce yace" mun tuntubi City akan dan wasan kuma a yanzu muna sauraronsu".

A sabon tsarin gasar premier dai, kowacce kungiya za ta zabi 'yan kwallo 25 wadanda zasu taka mata leda a gasar.

A halin yanzu dai Manchester City da Sunderland, daga nan zuwa ranar daya ga watan Satumba dole ne su yanke shawara akan Joe Hart.