Sudan na neman FIFA ta daga mata kafa

Shaddad
Image caption Gwamnati ta haramtawa Shaddad shiga zabe

Hukumar kwallon kafa ta Sudan ta bukaci FIFA ta karamata wa'adin makwanni biyu don ta gudanar da sabon zabe.

FIFA ta baiwa Sudan zuwa ranar 15 ga watan Agusta ta kara gudanar sabon zaben shugabanta ko kuma a haramtawa Sudan din shiga harkokin kwallo a duniya.

Hukumar kwallon Sudan a ranar talata ta yi taron gaggawa kuma ta amince da bukatar FIFA, amma dai ta son taji ta bakin ma'aikatar wasanni kasar.

Mutasim Jaafar ne aka zaba a matsayin sabon shugaban hukumar a ranar 26 ga watan Yuli.

Fifa dai ba ta jin dadin hukuncin gwamnati na haramtawa tsohon shugaban hukumar kwallon Sudan Kamal Shaddad, daga tsayawa a karo na uku.