Ayew zai cigaba da kwallo a Marseille

Ayew
Image caption Ghanian Midfielder Andre Ayew

Kungiyar Marseille ta Faransa ta ce dan kwallon Ghana Andre Ayew zai kulla sabuwar yarjejeniya da ita na tsawon shekaru uku.

Darektan kula da wasannin na Marseille Jose Anigo a ranar Alhamis yace Ayew ya amince zai kulla sabuwar yarjejeniya da zata sa ya cigaba a kungiyar har zuwa shekara ta 2014.

Marseille tace"abubuwa kadan suka rage a kamalla yarjejeniyar".

Ayew me shekaru 20, dan shahararen dan kwallon Ghana ne wato Abedi Pele,kuma kungiyar Stuttgart ta Jamus na zawarcinshi.

Ayew ya taimakawa Ghana ta buga wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika a watan Junairu da kuma zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya.